Labarai

Daga 2025 duk yaron da bai kai 18 ba ba zai shiga jami’a ba a Najeriya – Farfesa Tahir Mamman

Ministan ilimin Najeriya, Farfeasa Tahir Mamman ya bayyana cewa babu yaron da za a sake bari ya zauna jarrabawar kammala sakandire ba tare da cika shekaru 18 da haihuwa ba.

Farfesan wanda ya bayyana hakan yayin wata hira a shirin “Sunday Politics” ranar Lahadi na gidan talbijin na Channels, ya kara da cewa gwamnatin tarayya ta umarci hukumomin da ke kula da zana jarrabawar kammala sakandare ta WAEC da WASSCE da NECO da su bi sabon umarnin nata na kasancewar yara ƴan shekara 18 kafin cancantar zama a jarrabawar.

Ministan ya kuma ƙara da cewa sabuwar ƙa’idar ta shafi yaran da ke son zauna jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandare da ake kira UTME da hukumar JAMB ke tsarawa.

“Abin da muka yi a taron da muka yi da hukumar JAMB a watan Yuli shi ne mu fara aiwatar da wannan sabuwar dokar a shekarar 2025 domin bai wa iyayen yara isasshen lokacin shiri. Hukumar ta JAMB za ta tabbatar da cewa duk yaron da zai nemi gurbin shiga jami’a dole ne sai ya cika sharuɗɗan ƙasar na kasancewar ɗan shekara 18.” In ji ministan.
“Wannan ba sabon tsari ba ne. Tsari ne da ya daɗe.”

Kuma ai idan kuka ƙirga shekarun da ya kamata yaro ya kammala sakandare tunda daga shigarsa nazare zuwa firamare zuwa ƙaramar sakandare har ya kammala babbar sakandare, za su kasance 17 da rabi. Za su ƙarasa 18 lokacin da za su samu gurbin shiga jami’a”, kamar yadda ministan ya ƙara.

Ministan ya yi ƙarin haske dangane da shekarun da ya kamata kowanne yaro ya kwashe a makarantun kafin firamare da na firamare har zuwa kammala sakandare.

“Ya kamata yaro ya kwashe shekaru biyar na farko a makarantun nazare. Sannan a shekara shida ya kamata yaro ya fara makarantar firamare, inda kuma zai kwashe shekaru shida a firamare ɗin sannan ya wuce ƙaramar sakandare a shekaru 12 inda zai yi shekaru uku. Daga nan sai ya shiga babbar sakandare a 15, inda nan ma zai kwashe shekaru uku ko fiye da haka, daga nan kuma zai wuce jami’a yana ɗan 18.”

Daga ƙarshe ministan ya ce “daga yanzu hukumomin NECO da WAEC ba za su ƙyale duk yaron da bai kai 18 ya zauna jarrabawar kammala sakandare ba…”

BBC Hausa

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button