Labarai

BINCIKE: Barcin dare tsirara na ƙara yawan maniyyi ga namiji — Likitoci

Masana kiwon lafiya sun bayyana cewa yin barci, musamman tsirara na iya kara yawan maniyyin da maza ke samu ta hanyar baiwa ƴaƴan maraina damar samun iska.

Likitoci sun ba da shawarar cewa maza da ke da burin haihuwa su rika yin barcin dare tsirara domin hakan na haɓaka damar su ta samun haihuwa.

Likitocin sun yi nuni da cewa, wannan al’adar na iya inganta damar samun haihuwa ga maza, domin barin ƴaƴan maraina su sha iska da daddare an tabbatar da ya na ƙara yawan maniyyi.

A cewar wata cibiyar binciken lafiya ta Amurka, barin ƴaƴan maraina su sha iska na tasiri kai tsaye ga lafiyar maniyyi da ƙarfin ɗa namiji.

Bugu da ƙari, mujallar likitancin Amurka ta tabbatar da cewa yin barci tsirara yana taimakawa wajen kula da yanayin zafi mai kyau don lafiyar ƙwaya da ingancin maniyyi.

A jawaban su ga jaridar PUNCH Healthwise a cikin hirarraki daban-daban, ƙwararrun sun lura cewa matsatsun tufafi na iya haifar da zafi, suna mai jaddada cewa yanayin na bada gudunmawa sosai wajen lafiyar maraina wanda za a iya samu ta hanyar yin barci tsirara.

Wani farfesa a fannin likitanci da ilimin ‘endocrinology’ a kwalejin likitanci, Jami’ar Legas, Olufemi Fasanmade, ya bayyana cewa barci tsirara yana tasiri ga samun haihuwa.

Ga wani karatu ku saurara ga masu karancin maniyyi.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button