Labarai

Ba ma jin daɗi idan maza na kallonmu lokacin shayar da yara nono

Hukumar lafiya ta duniya ta ce rashin isasshen nonon uwa ga jarirai na haddasa mutuwar yara sama da dubu 800, a duk shekara, kuma hakan na kara barazanar kamuwa da cututtuka na dogon lokaci.

A yayin da a yau Laraba ake kammala makon shayar da yara nonon uwa na duniya, BBC ta tattauna da wata uwa take shayarwa a Abuja.

Matar ta shaida wa BBC irin kalubalen da take fuskanta a lokacin shayar da jaririyarta, idan ta bar gida.

Ta ce a duk lokacin da jaririyar take jin yunwa sai ta kebe domin ba ta nono, to amma duk da cewa tana sanye da hijabi da take lullube jaririyar ta shayar da ita, sai ta ga wasu maza na zura mata ido, wanda hakan ya sa ba ta jin dadi.

Matar da ƙara da cewa hatta wasu matan ma kan yi mata magana cewa, ”ke ba kya ganin yadda ake kallonki kina ba ta nono?” duk dacewa ta rufe jaririyar da hijabi.

Haka kuma ta ce tana fuskantar kalubalen gudanar da ayyukanta na gida da kuma shayarwa, inda a wani lokacin jaririyar na bukatar nono amma ita kuma ayyuka sun yi mata yawa.

Matar ta ce idan da za ta samu damar daukar ‘yar aiki hakan zai rage mata dawainiya.

Sannan ta bukaci jama’a da idan sun ga mace tana shayar da jariri a titi ko wani waje su rika tallafa mata a matsayin uwa domin abu ne da ya kama dole saboda yaro na jin yunwa, maimakon su riga tsangwamarta.

BBC Hausa

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button