Labarai

Ambaliyar ruwan sama ya raba titin Kano zuwa Maiduguri (hotuna)

Ambaliyar ruwan sama ya raba wani bangare na babbar hanyar Kano zuwa Maiduguri da ke Malori-Guskuri dake a karamar hukumar Katagum a jihar Bauchi.

An ruwaito cewa an samu tsaiko na bin hanyar, lamarin da ya tilasta wa masu ababen hawa yin amfani da wasu hanyoyin.

Da yake jawabi kan lamarin a ranar Alhamis, gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya jaddada mahimmancin hanyar, wadda ta kasance muhimmiyar hanyar sadarwa tsakanin sassan Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabashin Nijeriya.

Gwamnan ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta gyaran babbar hanyar da ta lalace domin saukaka zirga-zirgar.

Ambaliyar ruwan sama ya raba titin Kano zuwa Maiduguri (hotuna) Ambaliyar ruwan sama ya raba titin Kano zuwa Maiduguri (hotuna) Ambaliyar ruwan sama ya raba titin Kano zuwa Maiduguri (hotuna)

Domin kallon yadda wannan waje a cikin faifain bidiyo latsa nan. l

 

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button