Zanga-zanga: Tinubu ya amince da biyan N50,000 duk wata ga matasan yankin Neja Delta
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya amince da biyan N50,000 duk wata ga matasan yankin Neja Delta su 10,000 domin rage wahalhalun da kasar ke ciki.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ne ya bayyana hakan a yayin taron wayar da kan kabilu da matasa da mata na yankin Neja Delta a Fatakwal a ranar Talata.
Ya ce za a biya kudin ne a karkashin shirin Youth Intensive Scheme kuma zai dauki tsawon watanni 12 na farko tare da yiwuwar tsawaitawa, kamar yadda Dclhausa na ruwaito.
Wani Labari : MTN ya koma aiki bayan da ya rufe Ofisoshin sa a Nijeriya
Kamfanin sadarwa na MTN a Nijeriya ya koma aiki a duka fadin kasar bayan rufe Ofisoshin sa da yayi a ranar Talata.
Kullewar Ofisoshin nasu na zuwa ne bayan da kwastomomin su sukai masu barna, sakamakon katsewar masu layukan wasu wayoyi na rashin saka Lambobin Shaida na dan kasa.
A ranar Laraba ne kamfanin na MTN ya sanar da komawarsa aiki a shafin sa na X, inda ya tabbatar da cewa shagunan sa za su kasance a bude ga kwastomomi daga karfe 8:00 na safe zuwa 3:00 na rana.