Zanga-Zanga: Duk wanda ya ta da yamutsi, za mu yamutsa shi, abi doka da oda – Sufeton Yan sanda
Sufeto-Janar na ‘yan sanda (IGP), Olukayode Egbetokun, ya ce rundunar ‘yan sandan Najeriya za ta mayar da martani kan zanga-zangar da wasu ‘yan Najeriya suka shirya yi a ranar 1 ga watan Agusta “ta hanyar da ta dace”.
Egbetokun ya bayyana haka ne a ranar Talata a Abuja, yayin wata ganawa da shugabannin ‘yan sanda da suka kunshi jami’ai daga mukamin kwamishinonin ‘yan sanda zuwa sama.
Ya ce wannan ganawar an yibshine domin a raba bayanan sirri tsakanin rundunonin tsaron da kuma tsara shirin ko ta kwana, domin tsaron kasa da dukiyoyin al’umma.
” Saboda haka ina tabbatar muku a shirye muke don tabbatar da ganin an yi wannan zanga-zanga cikin lumana kuma jami’an tsaro za su yi aiki cikin kwarewa.
” Idan masu zanga-zanga suka fito cikin natsuwa da ta lumana, za ku ga mun samar musu da kariya.
“Amma fa idan zanga-zangar ya rikiɗebzuwa tashin hankali da fasa shaguna da ɓarnata dukiyoyin al’umma to nan fa ba za mu kyale ba.
” Za mu samar wa masu zanga-zanga kariya, idan suka fito cikin natsuwa da sanin ya kamata.
Leadershiphausa