Wata sabuwa : Nafisa Abdullahi ta bayyana dalilin da yasa bata son haihuwa


Jaruma Nafisa Abdullahi ta bayyana cewa duk da tana jin daɗin hulɗa da jarirai kuma suna bata sha’awa, to amma ba ta tunanin ta shirya haihuwar ƴaƴa na kanta saboda ba zata iya daukar nauyi da ƙalubalen da ke tattare da renon su ba.
A Yau ta ruwaito a wani saƙo da Jarumar ta wallafa a shafinta na tuwaita wato X, Nafisat ta nuna cewa “Ina son jarirai, ina son wasa da su kuma suna bani sha’awa to amma ba ni da juriya wajen rigimarsu, idan yaro ya rikice maka da rigima wani lokacin sai ka rasa ina zaka saka kanka. Don haka bana tunanin zan yarda na haifi jarirai na kaina… ” a cewar Jarumar
I adore babies, I love them but I have no tolerance for their crazy sides, lol they act like they’re possessed most times.
I don’t think I want babies of my own,nahhhh…I’ll pass ????
— Nafisat Abdullahi (@NafisatOfficial) July 21, 2024