Labarai

Masu garkuwa da mahaifiyar Rarara sun nemi a basu Naira miliyan 900 a matsayin kuɗin fansa

Ƴanbindiga da suka yi garkuwa da Hauwa’u Adamu, mahaifiyar fitaccen mawakin Hausa, Dauda Adamu, wanda aka fi sani da Rarara, sun bukaci a biya su kudin fansa har Naira miliyan 900m domin su sake ta.

Wata majiya ta kusa ta shaida wa jaridar Daily Trust cewa wadanda suka yi garkuwa da tsohuwar sun kira iyalin ta, inda suka bukaci a biya su Naira biliyan 1 da farko.kamar yadda daily Nigerian Hausa na ruwaito.

Majiyar ta ce: “Sun kira ‘yan uwa da wayar wata mata da suka karɓe a lokacin da suka zo daukar Hajiya.

“Sun bukaci Naira biliyan 1, amma bayan wata ƴar gajeriyar tattaunawa da wani dan uwa, sun rage kudin zuwa N900m.

“Da farko sun bukaci a kulla yarjejeniyar da Rarara da kansa amma suka canja saboda ya kamu da rashin lafiya bayan sace mahaifiyar ta.

“Sun amince da kulla yarjejeniya da wani dan gidan. Sun tabbatarwa yan uwan cewa Hajiya na cikin koshin lafiya kuma da zarar an biya kudin za a sako ta.

“Tun daga lokacin ba su sake yin waya ba. Amma na yi imani har yanzu ana ci gaba da tattaunawa. Don haka, har yanzu a na jiran kiran ‘yan fashin jejin don ci gaba da tattaunawa.”

 

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button