Labarai

LGBT:Prof Mansur Sokoto yayi martani akan Yarjejeniya da ake zargi Gwamnatin Najeriya tayi da SAMOA

Advertisment

An fara zargin gwamnatin tinubu ta kulla yarjejeniya da kungiyar SAMOA wanda ta kunshi harda madigo, luwadi, auren jinsi da maka mantan su akan.

Labarin ya fito ne daga jaridar Daily trust a safiyar yau din nan inda anka samu wani matashin harka doka Abdul-hadee Isah Ibraheem yayi tsokaci akan wannan doka abin da take nufi a fahimtarsa inda yake cewa.

Samoa Deal (Agreement):

Idan har ta tabbata cewa Gwamnatin Nigeria ta amince da Samoa Deal to sai dai muce Allah ya isa.

Advertisment

Rahotanni suna bayyana cewa Gwamnatin Nigeria ta amince ta Sanya hannu akan Samoa Deal, Ministan Budget and Economic Planning Atiku Abubakar Bagudu ya bayyana cewa Gwamnati ta Sanya hannu akai ranar 1 July 2024 bayan wakilan kungiyar hadin kan kasashen Turai sun zo Abuja (EU) ko “European Union”.

Samoa Deal, wata yarjejeniya ce da ta kunshi abubuwa da yawa, daga cikin akwai amincewa da dukkan aiyukan kungiyar LGBTQ wato (Lesbian, Gay, Bisexual, Transgender and Queer).
~ Ranar 15 November 2023 data gabata anyi wani taro a New York dake America inda aka gabatar da Samoa Deal Agreement ga kasashen duniya da dama, sai dai kasashe 35 sunki amincewa, ciki harda Nigeria, Nigeria taki amincewa saboda ya sabawa addini da Al-adun da ‘yan kasar suke bi.

Kwatsam sai jiya aka ji Ministan Budget Atiku Abubakar Bagudu yana cewa Gwamnati ta amince da hakan, da aka tuntube shi akan LGBTQ sai yace a’a babu maganar Madigo, Liwadi, Auren jinsi a cikin abinda suka sawa hannu.
~ Yace abinda sukawa hannu ya shafi tattalin arziki ne kawai na Dala Biliyan 150.

Wani wakilin Fadar Sarkin Musulmi yace an basu kwafin takardun masu shafi Dari 403 amma basu ga zancen LGBTQ a ciki ba, yace koda akwai toh su basa goyon bayan.

Yanzu haka zance ya fara tayar da kura a Nigeria.
Idan ba’a manta a lokacin Jonathan da lokacin Buhari an bijirowa Nigeria da zancen, duka Gwamnatocin suka yi watsi dashi.

Ko me yasa Gwamnatin Tinubu taki amincewa da yarjejeniyar a 2023 yanzu kuma ta amince?”

Shine babban malamin addinin Muslunci a Najeriya Farfesa mansur Ibrahim Sokoto mni yayi martani da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta yana cewa:

SAMOA: Ni fa abinda nake so shi ne masu fashin baƙi, ina nufin lauyoyi masanan harkar su karanta wannan yarjejeniyar su faɗa mana haƙiƙanin abinda ta ƙunsa, sannan mu fara ta da jijiyar wuya idan abinda ake tuhuma gaskiya ne sai mu ɗaga murya kuma mu kira shugabanninmu su sa baki don kada a jefa al’ummar mu cikin wani hali na lalaci da ba mu buƙata.
Faƙat”

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button