Kaji Rabo : Na haifi ‘ya’ya 100 duk da ban taba aure ba – cewar mai kamfanin telegram
Wanda ya kirkiri dandalin Telegram, Pavel Durov ya fallasa wani sirri mai ban mamaki game da haihuwar yara 100 da ya ce ya yi duk da bai taba yin aure ba.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Telegram din a ranar Litinin da yamma, dan kasuwan mai shekaru 39 ya ba da labarin yadda ya kai ga haihuwar āyaāya da dama, legithausa na ruwaito.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa kimanin shekaru 15 da suka gabata ne wani abokin Mista Durov ya tuntube shi a kan ya ba da gudunmawar maniyyinsa a asibiti.
An ce matar abokin ce ta gaza daukar ciki saboda wata matsala, inda suka nemi Mista Durov da ya ba da gudummawar maniyyinsa domin matar ta dauki ciki.
Da farko Mista Durov ya ce yana da shakku, amma daraktan asibitin ya shawo kan shi, wanda ya bayyana maniyyinsa a matsayin “mai inganci” da cewar yin hakan aikin jama’a ne.
Mista Durov ya bayyana cewa: āBa a jima da fada mani cewa cewa ina da yara sama da 100 ba, wadanda na haifa ta dalilin ba da gudunmawar maniyyina ga ma’auratan da suke gaza daukar ciki da kansu.” Ya bayyana cewa gudummawar maniyyinsa da ya bayar ya taimaka wa ma’aurata 100 a cikin Ęasashe 12 domin ba su damar rainon ciki da kuma goyonsa, inji rahoton The Cable.
Duk da cewa ya dauki shekaru bai ba da gudummawar ba, ya bayyana cewa har yanzu asibitin IVF yana da ragowar daskararren maniyyinsa domin amfani ga iyalai masu neman haihuwa.