Dole sai ka iya turanci iyayanka zasuyi alfahari da kai, kuma shugaban kasa baya da laifi – Fatima Hussaini “Maryam labarina


Shahararriyar jaruma masana’atar Kannywood fatima Hussaini wadda take haskakawa a cikin shiri mai dogon zango labarina Maryam matar Alhaji mai nasara a cikin shirin
Fatima Hussaini a cikin wani faifan bidiyo tana maganganu wadda sunka jawo cece kuce a kafafen sada zumunta inda take cewa.
“Turanci yare ne da ake amfani da shi a duniya domin iyashi shine zai sanya iyayenka su fara tunanin basu haifi matsiya ci ba, domin zaka iya kasuwanci daga dubai zuwa amerika kuma turanci zakayi ba hausa ba”
Fatima Hussaini ta kara da cewa
“Ilimi abu ne mai kyau idan baka da shi laifin ka ne saboda haka shugaban kasa bai da wannan laifi saboda basu fito sunka nuna baka aikin ka ba, saboda haka a daina ganin laifin tinubu akan abubuwan da yake faruwa a cikin kasar nan.”-inji fatima Hussaini
Ga bidiyon nan a saurara.