Labarai
Da Ɗumi-Ɗumi: Kamfanin MTN ya rufe ofisoshin sa a faɗin Najeriya


Advertisment
Kamfanin MTN ya sanar da rufe dukkan ofisoshin sa dake Najeriya daga yau Talata 30 ga watan Yuli.
Wani jami’i a kamfanin ne ya tabbatar da hakan ga jaridar TheCable.
Majiyar ta ce an ɗau matakin ne sakamakon farmakin da fusatattun mutanen da aka rufewa layuka suka kai wa kamfanin.
A ranar 27 ga watan Yuli ne dai ƴan Najeriya da dama suka kai kokensu bayan hana su amsa kira da yin kira a layukan nasu sakamakon rashin tantance lambar NIN dinsu.
A ranar Litinin ne wasu fusatattu masu amfani da layukan suka farmaki ofishin MTN dake Festac a jihar Legas.
Daily Nigerian Hausa
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)




