Bani da masaniya a kan dukan da aka yi wa Danbilki Kwamanda — Uba Sani


Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya nesanta kansa daga cin zarafi da aka yi wa wani jigo a jam’iyyar APC a jihar Kano, Abdul-Majeed Al Mustapha, wanda aka fi sani da Dan-Bilki Kwamanda.
A cikin faifan bidiyon da ke yawo a yanar gizo, an ga wasu da ba a san su ba su na zane Kwamanda bisa zargin zagin gwamnan jihar Kaduna
Sai dai a wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa, Muhammad Lawal-Shehu ya fitar a yau Alhamis, Gwamna Uba Sani ya nisanta kansa da wannan danyen aikin, yana mai cewa irin wadannan ayyukan cin zarafin ba shi da gurbi a cikin al’umma mai mutunci.
Shehu ya lura cewa gwamnan, wanda dan rajin kare hakkin bil adama ne, ba zai taba bada umarnin a ci zarafin wani saboda bambancin ra’ayi ba.
Gwamnan ya kuma ba da umarnin gudanar da cikakken bincike kan tushen lamarin, yana mai shan alwashin tabbatar da ganin an hukunta duk wanda aka samu da hannu.
Daily Nigerian Hausa