Labarai

Anzo inda ba’a so : Bidiyon Yan sanda sun cafke yaro dan shekara 13 yana baiwa yan bindiga bayyanan sirri

Advertisment

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina karkashin jagorancin CP Aliyu Abubakar Musa Psc, ta kama wani yaro (Al’majiri) ɗan shekara 13 da hannu dumu-dumu yana bai wa barayin daji bayanan sirri kan yadda suke satar dabbobi da kuma garkuwa da mutane zuwa daji don neman kudin fansa, a karamar hukumar Ɗandume da ke jihar Katsina.

Katsina Reporters ta samu cewa, Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ASP Abubakar Sadiq, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai, a wata zantawa da ya yi dasu a babbar Hediƙwatar ‘yan sandan da ke cikin ƙwaryar birnin jihar.

A cewar, Kakakin rundunar ASP Abubakar Sadiq, barayin dajin suna bai wa yaron Naira dubu biyar ko dubu ukku idan sun yi nasara a matsayin la’ada.

Ga bidiyon hirar nan da ankayi da shi.

Advertisment

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button