Kannywood
Allah yayiwa Mahaifin Garzali Miko Rasuwa
Advertisment
Innalillahi Wa’innah Alaihi Raj’un duk mai rai mamace a yau Allah yayiwa Mahaifin fitaccen mawakin nan Garzali miko rasuwa.
Garzali miko yayi jimamin rasuwa mahaifinsa sosai inda yake wallafa wasu kalamai na jimami na rashin mahaifinsa masu ratsa zuciya wanda tabbas rayuwar ɗa da mahaifi akwai ciwo akwai zafi kamar yadda ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.
“Tabbas Nayarda da kalmar nan da Hausawa suke fadi lokacin da wani yake cikin farin ciki lokacin wani yake rasa nasa farin cikin Nidai yau narasa nawa Allah yakai Haske kabarinka Baban mu”
A madadin CEO Hausaloaded da mabiyansa suna mika sakon ta’aziyya zuwa ga Garzali miko da yan uwansa jaje Allah ya gafartamasa yayi masa rahama amin.
Advertisment