Labarai

Ali artwork ya zargi madam korede da yi masa sata

Advertisment

Jarumin Barkwancin nan Ali Artwork da aka fi sani da Madagwal ya zargi Jaruma Maryam Korede ta Kaduna da dauke masa waya a taron da Dan Wasan Kasar nan Ahmad Musa ya hada don sada zumunta tsakanin Jarumai.

Sai dai Korede ta musanta zargin inda ta tabbatarwa da Freedom Radio cewa, zargin da Madagwal ya yi mata ba komai ba ne face kalen sharri.

Rahotonni sun ce har lamarin ya dangane da ofishin yan sanda hakan ya sa Freedom Radio ta tuntubi Kakakin Yansandan jihar Kaduna ASP Mansur Hassan sai dai ya ce, bai samu rahoton ba, amma zai bincika sannan ya bamu karin bayani daga baya.

Freedom Radio ta yi kokarin jin ta bangaren Malam Ahmad Musa da ya shirya taron kan zargin da Madagwal ya yi masa cewa shi ne ya karbi belin jarumar, sai dai hakanmu bai cimma ruwa ba.

Ga sautin murya madagwal nan ku saurara.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button