AddiniLabarai

Abubuwa biyu ne zasu sanya mutum yayi murna sace mahaifiyar Rarara – sheikh Ishaq Adam

Siyasa ta lalata mana zamantakewa, har murna ake idan musifa ta samu mutum

Malamin Addinin musulunci, Barista Ishaq Adam, ya bayyana rashin jin dadinsa akan yadda al’ummar musulmi ke murna idan wata musifa ta afkawa dan uwansu, kawai saboda saɓanin ra’ayin kwallon ƙafa, ko siyasa ko wata mu’amala.

Barista ya bayyana haka ne cikin wani bidiyo da aka wallafa a shafin Karatuttukan Malaman Musulunci a Facebook, inda ya bada misalin da sace mahaifiyar mawaƙin siyasa (Dauda Adamu Rarara), da yace ya ga wasu sai murna suke yi, wanda hakan ba koyarwa Addinin musulunci bane, a Addinin musulunci ana so duk abinda ya samu musulmi to dan uwansa musulmi yaji cewar kamar shi abin ya shafa.

Malamin ya ƙara da cewa, tsarin mulkin Demokradiyya ya sanya abubuwa sun lalace, wanda kamata yayi idan wata musifa ta samu mutum, a taimaka masa ko da addu’a ne, domin babu wanda ya tsira daga shiga irin wannan jarabawa.

Ga bidiyo nan.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button