Labarai

Ƙarya kike, ban taɓa kwana a gidan ki ba, Alkali Dandago ya faɗa wa Sadiya Haruna

Advertisment

Babban alkalin majistare a jihar Kano mai ritaya, Muntari Dandago, ya musanta ikirarin da wata shahararriyar mai sana’ar kayan-mata kuma ‘yar wasan kwaikwayo, Sadiya Haruna ta yi cewa yakan je gidanta ya ci abinci har ma ya sharara bacci.

Ya ce ikirarin wani yunkuri ne na ɓata masa suna.

A watan Fabrairun 2022, lokacin da Dandago ya majistere, ya yanke wa Sadiya Haruna hukuncin zaman gidan yari na tsawon watanni shida ba tare da zabin biyan tara ba saboda bata sunan tsohon mijinta Isa Isa.

Sai dai da ta fito a wani shirin hira da Hadiza Gabon ta ke shirya wa, wanda jarumar Kannywood Hadiza Gabon ta dauki nauyin shiryawa, Sadiya ta zargi Dandago da cin amanarta ne ta hanyar tura ta gidan yari duk da kasancewarsa abokanta.

“Abin takaici shi ne alkalin da ya tura ni gidan yari yakan zo gidana. Mukan zauna tare, mu yi hira, mu ci abinci… Wani lokaci ma yakan kwana a gidana. Amma a ƙarshen ranar, abin da ya faru ke nan. A ƙa’ida bai kamata ya zauna a shari’ar ba.

Da DAILY NIGERIAN ta tuntubi Dandago ya shaida cewa zargin ba shi da tushe balle makama, inda ya kara da cewa yana daya daga cikin kalubale da ma’aikatan shari’a ke fuskanta a yayin gudanar da ayyukansu.

“Ka ga wannan wani bangare ne na kalubalen da muke fuskanta a matsayinmu na ma’aikatan shari’a, mutane na tsoratar da ku ta hanyar yin yarfe, suna tunanin za ku giya musu baya.

“Wannan ba shi ne karon farko da ta yi irin wannan ikirarin mara tushe ba.

“Ko a lokacin shari’ar, ta fadi abinda ya fi wannan ma za ku iya zuwa ku tabbatar. Amma ban damu ba. Na san na gudanar da shari’ar da matuƙar ƙwarewa,” in ji shi.

Daily Nigerian Hausa

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button