Labarai

‘Yan bindiga sun aika fasinjoji da manoma fiye da mutane 17 barzahu a jihar Katsina

Akalla mutane 17 ne aka ce an kashe a wasu hare-haren ‘yan bindiga a kauyukan karamar hukumar Kankara ta Jihar Katsina.

Lamarin na baya-bayan nan wanda ya faru a ranar Alhamis, ya shafi fasinjojin wata mota kirar bas da ‘yan bindiga suka kai wa hari a kusa da kauyen Dan Marke da ke kan titin Kankara zuwa Marabar Kankara yayin da take dawowa daga kasuwa.

Majiyarmu ta Katsina Reporters ta ruwaito cewa Wani mazaunin garin ya shaida wa wakilinmu cewa mutane biyar ne suka mutu nan take ciki har da direban motar mai suna Dan Mashi, yayin da wasu da suka samu raunuka a dalilin harbin bindiga ke karbar magani a asibiti.

Ya kara da cewa, an sace biyu daga cikin fasinjojin ciki har da dan direban da ya mutu.

Har ila yau a safiyar ranar Alhamis an kashe manoma bakwai a gonakinsu a kauyen Katsalle kusa da Mabai a karamar hukumar Kankara.

Wani mazaunin garin wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce a farkon mako, ‘yan bindigar sun kuma kashe wasu manoma uku a gonakinsu yayin da suka sha alwashin ba za su bari manoman su yi noma a wannan kakar ba.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button