Kannywood

Ty shaba yayi martani akan kalaman hadiza Gabon da zaharadeen sani

Fitaccen jarumi a masana’atar Kannywood Ty shaba yayi martani da nazari a fahimtarsa na dan adama akan kalaman jaruma hadiza Gabon kamar yadda ya wallafa a shafinsa na sada zumunta @official_tyshaban

Ga abinda yake cewa

Hadiza Gabon Matsalar Al’umma Ta Kawo Bana Yanfim Ba

– zan ce koma gida kije kiyi karatu, aure da sauransu Saboda me?

– fata na zaku fara lafia ku gama lafia, nima naga alherin, shin akwai wani aibu ne ko rashinsa?

– ko wane lamari yana da advantage ko disadvantage, cikin advantage ko rashinsa wanne ya rinjayi wani a sana’ar fim? Hadiza bata fada ba did not mention any

– sai ka kai wani kololuwar mataki ‘pick’ za a zarge ka da abin da baka da ruwa ko laifi. Shin wannan lafinka ne ko na al’umma?

– wani abu ya sameka sai ace Danfim ne ko da kana da gaskiya ko babu. Shin akwai adalci anan?

– kina ji kina gani farin cikin ki zai zulle ba tare da dalili ba. Wannan ya nuna Yarfim mutuniyar banza ce?

A tunani na Hadiza lafazin ya kufce mata ne kuma take kokarin saisaita bayani domin kowa ya gane, saboda matsalar al’umma ta kawo bana Yanfim ba.

Ba wai wani sharri ne a cikin sana’ar fim ba, illa yadda wasun mutane ke kallon sana’ar a matsayin jagaliya ba tare da wani kwakkwaran dalili ba,

Wannan shine yasa Hadiza take gujewa mata har da samari shiga cikin HARKAR fim da zargin mutane yayi yawa akai,Domin Hadiza matsalar al’umma ta kawo bana yan fim ba.

A bangaren Zaharaddeen Sani kuwa ya zama dole mu yarda da cewa fahimta FUSKA ce, kowa da irin tasa. ALLAH YASA MU DACE.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button