Labarai

Talauci ko Rashin Imani: ya saki matarsa tana bisa gadon asibiti tana naƙuda ya gudu

Advertisment

Wannan Labarin ya faru akan idona, a Asibitin Mallam Aminu Kano, ranar Talata 25/06/2024, da misalin ‘karfe 5:30 na yamma, a farfajiyar ‘dakin masu haihuwa  (Labour Room):

Nurse: “Matar ka ba zata iya haihuwa ba, Likitoci sun ce a fa’damaka sai dai ai mata tiyata (CS)”.

Miji: “Caaab! Wallahi bazan iya biyan ku’din nan ba, sunyi yawa. Ya juya wajen Mahaifiyar ta da ‘yan uwan ta, “taje na sake ta saki uku”.

‘Yan Uwanta: “Innalillahi wa Innaa Ilaihi Raji’oon! To ai dama ka ta’ba yimata saki ‘daya.

Miji: “Eh, taje to wannan har na hudu ne”.

Ya tasa ‘keyar sa yai tafiyar sa. A gaban idon mu ‘yan uwanta suka fashe da kuka.

Allah kai mana tsari da zuri’ar mu da ‘yan iska!

Majiyarmu ta samu wanna labari Aysha  Mahmoud

Hira ta da Baban Bilkisu da Maman ta!

 

Ga Bilkisu, ga kuma ‘dan data haifa, a Lokacin da take na’kuda mijin ta ya sake ta.

Bilkisu bata da waya. Mahaifin ta da yake da ita kuma ta lalace. Na so ace na samu number sa, amma bai ri’ke ba. Na basu tawa, kuma sun yimun al’kawarin kirana a waya idan suka je gida, kasancewar yau aka sallame su.

Sun bayyana mun cewar a Gunduduwa suke da zama. Har i yanzu, shi Mijin Bilkisu bai tuntube suba. Kuma ko suna basu sakawa ‘dan ba.

Talauci ko Rashin Imani: ya saki matarsa tana bisa gadon asibiti tana naƙuda ya gudu

Talauci ko Rashin Imani: ya saki matarsa tana bisa gadon asibiti tana naƙuda ya gudu

 

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button