Shehin malami sheikh Ibrahim khalil a majalisin sa na karatu anyi masa tambaya cewa shin kirifto halal ne ?
Malam ya amsa tambaya inda yake mai cewa:
“Kirifto ya halata mana kai bakasan ana diploma, digiri ana mastas akan sa ba a jami’a , ai wanda bai san shi bane yake magana ae shi kirifto ana kwarewa akansa duk ko abin da ake kwarewa akan sa ai shikenan ya halatta.
Su masu cewa haram ne sun sanshi ne?
Malamai da suke na duniya suka ta rubuce rubuce in ka tambaye su shi sunje makaratun na kasuwanci sun binciki cewa ana yin karatu akan kirifto, har azo ayi diploma ko digiri akansa sun sani basu sani ba.
Duk wanda baisan abu ba yazo yayi hukunci akansa kuma ka bishi bakasan ana zuwa a karanta shi ba, ae halal tafi haram yawa mu’amala kam halal ce sai wadda Shari’a ta haramta, ko wadda illar ta karara ta fito a fili wadda kowa ya yarda illar ta gaba daya ta shafi kowa , dan haka kirifto halal ne.
Ga bidiyon nan ku saurari karin bayyani