Labarai

Mutane 30 Sun mutu A Harin ’Yan Bindiga A Katsina

Akalla mutane 30 aka kashe wasu da dama na karbar magani a Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Katsina, sakamakon harin ’yan bindiga a kauyukan Dutsinma da Safana.

Wasu ’yan bindiga a kan babura ne suka kai wa kauyukan farmaki a ranar Talata, kamar yadda kafar yada labarai ta Katsina Times ta bayyana.

’Yan fashin sun kai harin ne a kauyuka Tashar Kawai Mai Zurfi, Sabon Gari Unguwar Banza, Dogon Ruwa, Sanawar Kurecen Dutsi, Unguwar Bera, Kuricin Kulawa, Larabar Tashar Mangoro, Sabaru da kuma Ashata.

Aminiya ta ruwaito cewa,Sauran al’ummomin da abin ya shafa sun hada da Unguwar Ido, Kanbiri, Kunamawar Mai Awaki, da Kunamawar ’Yargandu da ke Karamar Hukumar Safana.

Har ila yau, a daren Laraba da safiyar Alhamis, maharan sun sake kai wa garuruwan Dogon Ruwa, ‘Yar Kuka, Rimi, Lezumawa, da sauran kauyukan da ke kusa da Safana da ke kan iyaka da Dutsinma.

Mazauna kauyuka sama da 15 ne suka tsere daga gidajensu, inda suke neman mafaka a garin Dutsinma da kauyen Turare sakakamkon harin barazanar ’yan.

Hare-haren ‘yan bindiga na kara kamari a wasu sassan jihar Katsina, inda a baya-bayan nan aka samu rahoton faruwar lamarin a yankunan Batsari, Kankara, Malumfashi da Faskari, kamar yadda aminiya na wallafa

Kokarinmu na samun karin bayani daga kakakin ’yan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya faskara, domin har ya zuwa lokacin kammala wannan rahoton, ba a samu lambar wayarsa ba, kuma bai masa rubutaccen sakon da aka aika masa ba.

Aminiya

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button