Sautin Murya : Bello Turji ya musanta kama Baleri da sojojin Nijar suka ce sun yi
Dan bindiga Baleri ya sake bayyana ‘yan kwanaki bayan da sojojin Nijar suka yi ikirarin kama shi
A cikin wani bidiyo, an nuna Bello Turji, yana daga hannun Baleri tare da musanta ikirarin kama shi, jaridar Dclhausa na wallafa a shafin su na sada zumunta
A cikin faifan sautin murya bello turji ne yake magana da yawun baleri cewa karya ne babu wanda ya kama shi ko an kashe shi ga abin da yake cewa
“Sunana Muhammadu bello turji wanda anka fi sani da a arewa maso yamma a kwana nan naji wani labari na fita daya bayan daya wasu mutane suna cewa suna kashe mutanen su suna zaluntar su suna cewa wai sun kama wani shi laftanal kanal baleri , to muna rokon mai girman Abdul Rahman thani talakawan nijar basa cikin wannan tsari yabar cutar da su.
Kada suma su fusata su kai ga dauka makamai kamar yadda muma mu ka dauki makamai.
Yanzu kaga muma a haka anka fara a Nijeriya aje a samu talakawa a kashe su ace an kashe yan bindiga , to an ce an kashe baleri an kama baleri wanene. To ga fa balerin.-inji bello Turji
A ciki zaku ji yana cewa gani fah, gani ga filin Allah hwa, wanda duk yasan baleri ya duba yagani.
Ga sautin murya da zaku saurari audio din.
Ga bidiyon da zaka kallo kai tsaye.