Matsalar tsaro : Ƴan Bindiga Sun Yi Gakuwa da Mahaifiyar Rarara
Kahuta, Katsina – Wasu ƴan bindiga sun shiga garin Ƙahutu da ke ƙaramar hukumar Ɗanja a jihar Katsina, sun yi garkuwa da mahifiyar Dauda Kahutu Rarara.
Rahotannin da Legit Hausa ta samu da safiyar ranar Jumu’a sun nuna cewa maharan sun ɗauki mahaifiyar fitaccen mawakin siyasar jiya Alhamis da daddare.
Mazaunan Kahutu sun bayyana cewa ƴan bindigar na ɗauke da manyan bindigu lokacin da suka shiga garin don haka ba a iya tunkararsu ba.
Ganau sun ce maharan sun kutsa sabon gidan da Rarara ke ginawa a garin Kahutu da karfe 1:00 na dare, suka yi awon gaba da datijuwar, Hajiya Halima Adamu.
Ana zargin dai ƴan bindigar ba su zo da abin hawa ba, kuma duk da sintirin da ƴan banga ke yi a garin, maharan sun ɗauki dattijowar ba tare da fuskantar turjiya ba.