Labarai
Mai kula da Dakin ka’aba Dr. Saleh bin Zain Al-Abidin Al-Shaibi ya rasu


Advertisment
Babban jagora mai kula da dakin Allah Ka’abah ya rasu, Dr. Saleh bin Zain Al-Abidin Al-Shaibi
Ya rasu yana da Shekaru 109 ya shafe shekaru 77 yana hidimtawa Ka’abah.
Ya fito daga kabilar Shayb daga gidan Qusay bin Kilab, Zuri’ar su ce ke rike da makullin Ka’abah tun zamanin Jahiliyya har zuwan Manzon Allah S. A. W.
An sami takardama bayan fatahu Makka wanda har Allah ya saukar da Ayar Al Qur’ani dake goyon bayan kabilarsu akan mayar da makullin zuwa ga ɗan kabilarsu..
Wanda hakan yayi silar shigar da yawa daga cikin yan kabilarsu addinin Musulunci.
Allah ya karawa Annabi Daraja. Ku taya mu yada Alheri shima sadaka ce..