Labarai

Ina mamakin yadda ake cece-kuce da rubuce rubuce akan ƙarin aure na – Sheikh Alkali Zaria aria

Advertisment

Shehin Malamin nan Alkali Abubakar Salihu Zaria ya ce yawan yabon da ya ke yiwa uwargidansa Jamila ba zai hana shi auren Sumayya ba.

A wata hira da Freedom Radio, ya ce auren da zai kara zai ragewa Jamila ayyukan gida sannan idan Allah ya amshi ransa ba ita kadai za ta ji zafi ba, haka kuma idan ita ta riga shi zai samu saukin radadi.

Ya ce, masu rubuce-rubuce kan aurensa a Social Media su sani babu abin da zai canja kuma ita Jamila kishinta irin wanda shari’a ta yarda da shi ne.

Malamin ya kuma ce, yabon da yake wa Hajiya Jamila yana nan daram ko gobe, haka ma karin auren mutuwa ce kawai za ta hana.

Advertisment

Freedom Radio ta tambayi Malamin ko daga Sumayya an rufe kofa?
Za kuji amsar da Malam ya bayar.
Muma daga nan Muryar Jama’a Muna yiwa Malam Fatan Alkhairi, Allah ya bada zaman lafiya.

“Tabbas na dade ina yabon jamila a cikin karatu saboda kyawawan dabi’u da kyawawan halayenta domin karin aure umurni ne na Allah (S W.T) da kuma sunnah ta Annabi Muhammad (s.a.w) soyayya ta kansa ka karowa mace abokiya zama dan tausaya mata , bisa dawainiyar abubuwa na yau da kullum na raguwa da tunanin kuma ko ni Allah ya karbi rayuwata zata dan ji saukin radadin ta ita kadai bace ko ni, ko idan Allah ya karbi rayuwata zan ji saukin radadin mutuwar ba ita kadai bace, wannan shine dalilina na kara aure. – inji sheikh alkali zaria.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button