Labarai
Hisbah ta cafke Lawancy ɗan TikTok mai rawar baɗala
Advertisment
A ci gaba da sumamen tsaftace kafafen sada zumunta da Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta soma ta cafke matashin nan Rabi’u Sulaiman da aka fi sani da Lawancy.
Hisbah na zarginsa da ci gaba da raye-rayen baɗala da riƙe hannun mata a bidiyo.
Idan za ku iya tunawa ko a shekarar 2023 ma Hisbah ta taɓa kama shi, amma ya nemi afuwa ya ce ya tuba.
Wadannan na kadan daga cikin bidiyo da yake yi da mata yana tabin jikin su a bainar jama’a.
Advertisment