Labarai
Gwamnatin Sakkwato na shirin tsige sarkin Musulmi – MURIC
Advertisment
Wani labari da munka tashi da shi a sayin safiyar nan ta majiyar Jaridar Daily Tust ta rawaito wata kungiyar kare ƴancin musulmi na zargin wani shiri da gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu ke yi na tumbuke Sarkin Musulmi Alh. Sa’ad Abubakar III.
Daractan kungiyar kare ƴancin Musulmin ta Muslim Right Concern MURIC wato Farfesa Isiaq Akintola ne ya bayyana haka a wata sanarwa.
Wannan raɗe-raɗi na zuwa bayan da gwamnan jihar Sokoto ya tumbuke masu rike da sarautar gargajiya a matakai daban-daban sama da mutum 15 tun bayan rantsar da shi.
Kuma wannan ya zo daidai lokacin da ake tsaka da dambarwar sarauta a Kano tsakanin Sarki Muhammadu Sunusi II da Alh. Aminu Ado Bayero.