Labarai
Davido Ga iyayen Chioma: Zan riƙe ƴar ku da kyau
Advertisment
Tauraron mawaki, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya tabbatar wa iyayen matarsa cewa zai riƙe ta da kyau da kuma mutunta ta wa.
A wani faifan bidiyo, an ga Davido ya durƙusa a gaban surukansa a yayin bikinsa da ke gudana a Legas.
Sai limamin da ke jagorantar auren ya nemi da Davido ya nemi auren ƴar su daga wajen su, kamar yadda al’ada ta tanada.
“Faɗa mana yadda za ka kula da ita domin mu ajiye a rubuce, ka san ka yi waƙa game da haka kuma ka sha magana a kan shi,” in ji ta.
Advertisment
Sai shi kuma Davido ya rusuna a gaban ta ya ce “ina da kalmomi biyu, su ne Zan riƙe ta har karshen rayuwa.
Sai kowa da ke wajen ya bushe da dariya.