Labarai
Ƴan bindiga sun kai ƙazamin hari masallaci, kashe sun dauki bayin Allah a Jihar Zamfara
Advertisment
Wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun kai farmaki wani masallaci a ƙauyen Tazame da ke karamar hukumar Bungudu a jihar Zamfara.
Rahotanni daga yankin sun nuna cewa maharan sun kai harin ne a daidai lokacin da mutane ne shirye-shiryen sallar asubahi ranar Talata, majiyarmu ta ruwaito daga legit.
Wani mazaunin kauyen ya shaida wa gidan talabijin na Channels cewa ‘yan bindigar sun far wa mazaunar kauyen ne a lokacin sallar asuba.
Advertisment
“Ƴan bindigar sun shiga kauyen suka kashe mutum biyu, ladanin Masallaci da kuma ƙaninsa,” in ji shi.
Ya kara da cewa maharan sun kuma harbi limamin masallacin wanda ya samu karaya a kafarsa tare da yin awon gaba da mutum kusan 10, PRNigeria ta ruwaito.