Tsohon mijin fatima mai zolage ya magantu akan ta dawowa ‘ya’yanta


Tsohon mijin fatima Aliyu wanda anka fi sani da Fatima mai zolage da shahararren mawakin nan dauda kahutu Rarara yayiwa waka yayi magana akan tsohuwar matarsa.
A cikin faifan bidiyo inda yake bayyana cewa yana rokon fatima da ta duba irin yadda yayansu suke kanana da ta dubi girman Allah ya dawo domin ta reni yayansu.
” Idan Allah yayi zan iya dawo da ita a matsayin matata badan komai ba saboda yaran nan“-inji tsohon mijin fatima mai zolage
Mijin yace shekarar mu biyu rabuwar mu da ita kuma tun a lokacin bata sake yin aure ba, wata hudu da na wuce taso tsohon mijin ta ya dawo da ita, kafin rarara yayi mata waka.
Abin da yasa tsohon mijin fatima mai zolage bai dawo da ita ba.
” Eh to a lokacin munyi magana da mamar ta da ita idan anka cemin kafin azumi da sati biyu, inyi kokari in kawo sadaki a daura muna aure da ita wannan azumi da ya wuce, maganar da munkayi anyi wata hudu 4 , kafin azumi za’a daura aure, sai kuma Allah da ikonsa bai yarda ba “- inji tsohon mijin fatima.
Sai dai manema labarai sun tambaye shi, shin daman kai ne za’a daurawa aure da fatima da take cewa zatayi aure, mijin yace a’a domin ya kasa hada abubuwan da ya dace yace a ɗaga masa kafa tace a’a an matsa mata a gida, saboda haka idan ta samu wani zatayi aure.