Labarai

Sojojin Najeriya sun hallaka ƴan ta’adda 227 tare da kame 529 cikin mako ɗaya

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun kashe Ƴan ta’adda 227 tare da kama wasu 529 yayin wasu samame da suka kaddamar a sassan ƙasar da dama cikin makon da ya gabata.

Wasu sojojin jamhuriyar Nijar da ke taimakawa Najeriya wajen yaki da kungiyar Boko Haram.

Wasu sojojin jamhuriyar Nijar da ke taimakawa Najeriya wajen yaki da kungiyar Boko Haram.

Daraktan yada labarai na rundunar Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai ranar Alhamis a Abuja.

Jami’in ya ce dakarun ƙasar sun kama wasu barayin mai 11, tare da kubutar da mutane 253 da aka yi garkuwa da su.

Makaman NATO

Sojojin sun kwato makamai iri daban-daban har 231 da alburusai 6,441, da sauran kayayyakin yaki ciki harda na NATO.

Daraktan ya bayyana cewa, rundunar sojin kasar na ci gaba da gudanar da ayyukanta a filayen daga daban-daban a fadin kasar, tare da maida hankali wajen kawo ƙarshen ayyukan ƴan bindiga, Boko Haram da barayin Mai da sauran ƴan tsageru.

Buba ya ce sojojin na yaki ne a cikin wani yanayi na kalubalantar yaki da ta’addanci kuma sun samu gagarumin ci gaba a yakin.

Ya kara da cewa, duk da irin nasarorin da aka samu, akwai sauran aiki a gaba, domin ana bukatar kawo ƙarshen ‘yan ta’adda musamman yadda suka maida hankali wajen farautar manyan kwamandodin su, tare da ayyana wasu a matsayin wadanda take nema ruwa a jallo.

Liberty yMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button