Sheikh Daurawa ya bayyana yadda jami’an gwamnati sunka fitar da Murja kunya


Babban Kwamandan Hisbah na jihar Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana yadda wasu jami’an Gwamnati da ya ce ba sa kaunar aikin Hisbah suka shiga suka fita aka ba da belin Murja Ibrahim Kunya.
A hirarsa da shirin Barka da Hantsi na Freedom Radio ya kuma bayyana yadda jami’an suka rika bita da kulli don bata hukumar ta Hisbah a wajen Gwamna Engr. Abba Kabir Yusuf.
Sheikh Aminu Daurawa yana cewa
” A cikin ko wace gwamnati akwai waɗanda basa son hisbah suka ɗebi waɗannan bidiyoyi sunka aje lokacin gwamna yana harka Shari’a hankalinsa bai ma zo kan abin da ake ba sai sunka aje, sai da munkayi samamin kamun murja aka kaita kotu, suka je sunkayi “prison break” sunka fidda murja.
Ana cikin Kano ta dame bayan gwamna yaje umrah sunka tura masa bidiyoyin abubuwan da sunka faru tun can baya, a matsayin ka na shugaban an tura maka bidiyo an gutsare ana dukan jama’a dole hankalin ka ya tashi, kuma hisbah ba irin aikin da suke ba kenan- inji sheikh Daurawa
Yadda anka jima yan Hisbah rauni anka fafashe musu kai.
Yanzu akwai bidiyon da idan na dauko maka yadda anka jima yan hisbah kai anka fafasa musu kai sai da munka kai su asibiti ankayi musu ɗinki, mun kace kada mu nuna wannan bidiyo saboda iyalinsu kada hankalin su ya tashi ko mutanen gari zasu ji haushi kada su ce sai sun ramawa yan hisbah din sai munka boye wannan sai kuma su sunka fidda wancan suka turawa gwamna suna masa bayyanin har sun ka dora shi ya tunzura.
To a lokacin dai Allah ya ƙaddari abun zai faru da yakamata ya kirani malam daurawa abubuwa kaza da kaza na faru a hisbah kaga sai naje nayi masa bayyani, ko yace kai SSG jeka ka zauna da malam ko shugaban ma’aikata jeka ka zauna da malam, ko mataimakin gwamnan jeka ka zauna da malam, saboda ni ya naɗa a matsayin wakilinsa a hisbah- inji sheikh Aminu Daurawa.
Malam yayi maganganu da yawa da zaku saurara a cikin wannan faifain bidiyo.