Labarai

Sauƙin sai ALLAH: Farashin Kayan abinci na tashin Gwauron zabi a wasu kasuwannin arewancin Najeriya

Farashin kayan Abinci sauƙi sai ga Allah a kasuwannin jihar Katsina kamar yadda majiyarmu ta samu rahoto daga Katsina post.

Tabbas yadda farashin abinci yake tashin Gwauron zabi dole a dukufa wajen addu’a sauki da damina mai albarka a kasar nan.

Kasuwar garin Dandume, ga yadda farashin sa yake kamar haka;

1- Buhun masara fara – 72,000 ja – 75,000
2- Buhun Dawa – 68,000
3- Buhun Gero – 75,000 Dauro – 75,000
4- Buhun Gyada tsaba – 115,000 Mai bawo – 47,000 ja – 155,000
5- Buhun Shinkafa tsaba – 130,000 samfarera – 50,000 ta tuwo – 150,000
6- Buhun Wake – 115,000 ja – 125,000
7- Buhun waken suya – 70,000
8- Buhun Dabino – 170,000
9- Buhun Tattasai – 50,000 kauda- 120,000
10- Buhun Albasa – 30,000
11- Buhun Alkama – 80,000
12- Buhun Makani – 45,000
13- Buhun Taki kamfa – 45,000 yuriya – 33,000
14- Buhun Barkono – 80,000 Dan zamfara – 90,000

Kasuwar garin ‘Yarlaraba a karamar hukumar Malumfashi,ga yadda farashin sa yake kamar haka;

1- Buhun Masara Fara – 70,000 ja – 72,000
2- Buhun Dawa ja – 65,000 Fara – 62,000
3- Buhun Gero – 65,000
4- Buhun Dauro – 66,000
5- Buhun Shinkafa tsaba – 154,000 shenshera – 118,000 ‘yar yarima – 114,000
6- Buhun Gyada tsaba – 125,000
7- Buhun Wake manya – 120,000
8- Buhun waken Suya – 71,000_72,000
9- Buhun Alkama – 78,000 _ 79,000
10- Buhun Albasa – 48,000 _ 49,000
11- Buhun Dankali – 44,000
12 Buhun Barkono – 77,000
13- Buhun kalwa wadda ba wankakka ba – 52,000
14- Buhun Sobo ja – 28,000
15- Buhun Fara – 45,000
16- Buhun kwaki – 86,000
17- Buhun Alabo – 68,000

Kasuwar garin Bindawa, ga yadda farashin sa yake Kamar haka;

1- Buhun Masara – 74,000
2- Buhun Dawa ja – 72,000 Fara – 72,000
3- Buhun Gero – 70,000
4- Buhun Shinkafa – 140,000
5- Buhun Gyada tsaba – 125,000 samfarera – 45,000
6- Buhun Wake manya – 130,000 kanana 120,000
7- Buhun Waken suya – 80,000
8- Buhun Tattasai danye – 40,000 Kauda – 100,000
9- Kwandon Tumatur – 15,000
10- Buhun Tarugu – 72,000
11- Buhun Garin kwaki ja – 44,000 fari – 52,000
12- Buhun Alabo – 54,000
13- Buhun Dankali – 40,000
14- Buhun Barkono – 85,000
15- Buhun Albasa – 35,000

Kasuwar garin Kankia, ga yadda farashin sa yake Kamar haka;

1- Buhun Masara – 78,000
2- Buhun Dawa – 72,000
3- Buhun Gero – 70,000
4- Buhun Shinkafa tsaba – 140,000
5- Buhun Gyada – 140,000
6- Buhun Wake – 120,000_130,000
7- Buhun Waken suya – 66,000
8- Buhun Alabo – 65,000
9- Buhun Alkama – 72,000
10- Buhun Kalwa – 52,000
11- Buhun Kwaki – 79,000
12- Buhun Sobo – 15,000
13- Buhun Aya manya – 68,000 kanana – 52,000
14- Buhun Dankali – 50,000
15- Buhun fara – 59,000
16- Buhun Ridi – 170,000
17- Buhun Tarugu – 70,000
Kara ta dabbobi
1- Rago – 370,000_350,000
2- Tunkiya – 65,000
3- Dan Akuya – 60,000

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button