Sauƙi sai Allah : Kayan Miya sunyi tashin Gwauron zabi
A zantawar mai kayan miyar da Dala FM Kano, ya ce ko a yau sun sayi buhun tattasai a kan Naira dubu 44, yayin da kwandon Tumatur kuma ya kai Naira dubu 70, inda suka sayi Attaruhu duk buhu kore dubu sittin, sai kuma jan Attaruhu buhu Naira dubu 80.
Malam Musa mai kayan miya ya ƙara da cewar tsadar kayan miyan yana da alaƙa ne da ƙarin kuɗin sufuri da aka samu, da kuma janye tallafin man fetur tunda masu noman rani suna amfani da inji wanda shi kuma fetur ake zuba masa.
Shima wani magidanci da ya je sayan kayan miya ya shaidawa Dala FM Kano, cewa, ya sayi Tattasai kowanne ɗaya akan Naira Ɗari, yayin da ya sayi Tumatur a kan kudi Naira saba’in-saba’in, sai kuma Attaruhu kore Naira goma duk guda ɗaya, yayin da ya sayi jan Attaruhu a kan guda biyu Hamsin.
Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il ya ruwaito cewar, mutane da dama ne suka rinƙa zuwa sayan kayan miya a wajen mai kayan miyar da ya je wajen sa, sai dai kuma da zarar an basu sai su tafi suna guna-guni da cewar ya yi musu tsada.