Neman taimako : Mata mai shekaru 46 ta haifi ƴan-huɗu
Wata Malamar makarantar sakandare, Sabina Mamah ta haifi ƴaƴa huɗu rigis bayan shekaru 14 da yin aure.
Sai dai kuma ta yi kira ga ƴan Nijeriya masu kishi da su taimaka mata.
Misis Mamah, wacce ta fito daga Obollo Orie a karamar hukumar Udenu a jihar Enugu, ta haifi maza uku da mace ɗaya.
Ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa cewa a halin yanzu tana Asibitin Koyarwa na Jami’ar Najeriya, UNTH, da ke Enugu kuma bata ga biyan kuɗaɗen da asibitin ke bin ta ba.
“Na ɗauki ciki a wajejen Oktoba 2023 kuma bayan an duba mini, sai aka gaya mini cewa ina dauke da ƴan-huɗu hudu.
“Don haka na yi rajista a UNTH don samun haihuwa kuma na haihu a ranar 23 ga Afrilu, ta hanyar tiyata, (CS).
“Ni malamar makarantar sakandare ce yayin da mijina Christopher, direba ne. Ni da jariraina muna tsare a asibiti saboda ba a biya kud’i ba,” inji ta.
Matar mai shekaru 46, ta ce ta yi aure ne a 2010 amma bata sami ciki ba sai yanzu.
Ta ce yanzu haka asibitin na bin ta cikin Naira 40,000 bayan ta samu wani bawan Allah Ya biya mata Naira dubu 600 kuɗin magani dqa haihuwa a asibitin
Daily Nigerian Hausa