Labarai

Najeriya ta karbi rancen da ya kai naira triliyan 11 a cikin watanni 4 Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta karbi rancen kudaden da suka kai naira triliyan 11 ta hanyar gwanjon takardun bankuna da ake kira ‘bond’ a cikin watanni 4 da suka gabata.

Wani bincike da Jaridar The Punch da ake wallafawa a cikin kasar ta yi, yace rahotan Babban Bankin Najeriya na CBN da ofishin taskance basussukan da ake bin gwamnati na DMO suka wallafa ya nuna cewar, gwamnatin ta karbi naira triliyan 3 ta hanyar bond da kuma naira triliyan kusan 8 ta hanyar takardun da ake kira ‘Treasury Bills’ na bankuna daga watan Janairu zuwa karshen watan Afrilun wannan shekarar.

Wannan mataki ba wani sabon abu bane dangane da hanyoyin da gwamnatoci kan yi amfani da su wajen samun kudaden tafiyar da ayyukan su, musamman a irin wannan lokaci da kudaden da gwamnatin ke samu suka ragu da kuma irin dimbin kudin ruwar da take biya sakamakon bashin dake kan ta.

Yanzu haka darajar kudin kasar na naira na ci gaba da faduwa, inda ake sayar da dalar Amurka guda tsakanin naira 1,250 zuwa 1,400 a kasuwannin bayan fage.

Faduwar darajar kudin kasar ya haifar da matsaloli sosai a kan tattalin arzikin Najeriya, musamman ga masana’antun da suka dogara da shigar da kaya kasar da kuma bangaren samar da abinci.

Rfihausa

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button