Matar Aure ta hallaka mijinta ya rasa ransa saboda yawan saduwa “Jima’i”
Wata matar aure mai shekaru 29 mai suna Torkwase Kpile ta daba wa mijinta wuka har lahira, bayan gardama ta barke a tsakaninsu saboda yawan jima’i a kauyen Achusa da ke karamar hukumar Makurdi a jihar Benuwe.
LEADERSHIP ta samu labarin cewa ma’auratan da suka yi aure watanni biyu da suka wuce, sun samu sabani kan yawan jima’i kafin matar ta dauki wuka ta daba wa mijin nata a wuya.
An bayyana cewa ta daba wa mijin nata mai suna Igbah Kpile, wuka a sassa da dama na jikinsa wanda daga bisani rai ya yi halinsa.
Ihun da mijin ya yi shi ya jawo hankalin makwabtansu, wadansa suka shiga gidan suka tarar da shi kwance cikin jini.
Tun da fari matar ta yi korafin cewar mijin nata yana yawan damunta da jima’i, wanda har ta kai da ta fara gajiya.
Ko da yake an garzaya da shi wani asibiti da ke Makurdi, amma kafin a karasa ya rasu.
Tun bayan faruwar lamarin, matar ta tsere kuma ‘yansanda na nemanta ruwa a jallo.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto mun kasa jin ta bakin kakakin rundunar ’yansandan jihar, SP Catheren Anene, domin karin haske kan lamarin.