Labarai

Kishi kumallon mata : Amatya ta ƙone hannayen ‘ya’yan kishiyarta biyu

Advertisment

Ƴansanda sun cafke Rachel Geoffrey mai shekaru 23 bisa zarginta da laifin ƙona hannun ƴaƴan uwargidanta biyu a jihar Adamawa

Rachel, na zaune ne a gidajen gwamnatin tarayya da ke Girei, ta yi sanadiyyar jin munanan raunuka a kan Genesis Geoffrey mai shekaru 7 da Ijadai Geoffrey mai shekaru 3. Da ma dai mahaifiyar yaran mai suna Rahila ta rabu da mahaifinsu a baya.

Rahotanni sun ce Rachel ta fusata ne bayan da yaran suka cinye abincin mahaifinsu da ta dafa ta ajiye masa. Daga nan ne ta ɗaure hannayen nasu da kyalle kafin ta cinna musu wuta.

Kishi kumallon mata : Amatya ta ƙone hannayen  'ya'yan kishiyarta biyu
Kishiyar da ta ƙone hannayen ‘ya’yan abokiyar Zaman ta biyu

Kwamishinan ƴan sanda na jihar Ɗankombo Morris ya shawarci iyaye da su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu kana ya kuma ba wa jama’a tabbacin yin bincike sosai kan lamarin.

Leadership Hausa

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button