Labarai

Gwamnatin Buhari da ta shuɗe bata da Hannu A kalubalen da muke fuskanta A Halin Yanzu – Kashim Shettima

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya jaddada cewa Gwamnati mai ci zata dauki dukkan nauyin kalubalen da ta fuskanta tun bayan hawanta karagar mulki, ba tare da dora laifin a kan Gwamnatin da ta Gabata A ƙarƙashin jagorancin Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ba.

Da yake jawabi a taro na biyu na Tarihi na karni na 21, Mataimakin shugaban kasar ya bayyana irin wahalhalun da ke tattare da shugabanci a fagen siyasa a Najeriya a cikin matsalolin da ƙasar ke fuskanta.

Yace, “Mun ki da zargim Gwamnatin da ta gabata, Saboda shugabanci na bukatar jajircewa akoda Yaushe.”

“Kafin Mu hau kan karagar mulki, wani babban batu shi ne cire tallafin man fetur, wanda ya yi wa al’ummar kasa nauyi tsawon shekaru 20 zuwa 30. Mun fahimci wajibcin wannan shawarar da magabatanmu ya yanke, Ganin rashin isassun tanadin kasafin kudin tallafi.”

“Shekara ɗaya Gabannin wa’adin mu, bashin da ake bin Najeriya ya ƙaru zuwa kashi 111.18 cikin 100, Wanda hakan ya haifar da babbar barazana ga tattalin arziki.

“Dole ne mu yi watsi da tsarin Tallafin, ba tare da son rai ba, tare da la’akari da shi a matsayin mai ɗaci amma dole ne a haɗiye.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button