Gaskiyar labarin abin da ya faru da satar ƴara da ƴar sanda tayi daga Sokoto zuwa Abuja
Labarin satar yara da wata yar sanda tayi daga jihar Sokoto zuwa abuja domin ta sayar da su, wani mai amfani da kafar sada zumunta ta Facebook justice Naseer ya bada labarin yadda abun ya faru kamar haka.
Wani bawan Allah da ke tashar ALU da ke birnin Sokoto mai suna babangida, shine wanda ya dauki wannan matar yar sanda wadda ta sace daga Sokoto zuwa abuja wato ASP Elizabeth.
Tun Suna Kan Hanya Sun Tsaya Lalan Dake Jahar Zamfara aci abinci mutane sa ke cikin motar suka kirashi gefe suka cemai gaskiya sudai basu yadda da wannan matar ba saboda ansawa yaran Kayan Inyamurrai Amma Kuma Hausa Kawai sukeji sannan kuma ita wannan jaririyar mai sati biyu da haifuwa kuka kawai takai cikin motar ance ta bata nono amma sai madara kawai taketa dirkawa jaririyar.
shigar direbar cikin mota ke da wuya sai ya mata magana kan maganar da fasinjoji sukayimai akanta, sai tace wallahi abin da suke tunani ba hakan bane duk yaran biyar diyan tane, direban yace kina kiristan taya zaki haifi diya hakan babu ko shekara duk tsakaninsu abun kamar malam bahaushe.
Shigarsu abuja keda wuya kawai baiyi birki ta ko ina ba sai police station, yan sanda sunyi sunyi ta fadi gaskiyar ya diyan suke, taki amma da tasha mari kawai sai ga bayani ya fara fitowa bakinta na cewa wallahi diyan ta sato sune daga Sokoto,kuma zata sai dasu nan Abuja.
Kan Dubu Dari Takwas ₦800,000 duk namijin daya, macce Kuma kan naira miliyan ɗaya ₦1million.
Amma Alhamdulillah ansamu kamasu yanzu hakan rikicin ya dawo hannun gwamnatin jihar sokoto, an samu nasarar kuɓutar da yaran.