CBN ta janye daga karawa Yan Najeriya harajin kuɗi bisa umarnin Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu bayan dawowarsa daga godon tafiya ya tarar da wani umarnin Babban Bankin Najeriya na CBN na shirin karawa Yan Najeriya kuɗi, kaso 0.5
Sai dai Shugaban Tinubu ya nuna rashin jin dadinsa tuni ya tura umarni akan Babban Bankin Najeriya CBN ya sauka daga kan wannan kuɗiri na karawa yan Najeriya haraji a bankuna don samar da tsaron yanar gizo.
Tinubu ya bayyana cewa, wannan tsari na babban Bankin kasa bai da ce da wannan lokacin ba, saboda halin da Yan kasa ke ciki a Yanzu. Inji Tinubu.
Wani labari: Iftila’in da ya faru da tsohuwar jaruma Maryam Wazeery “Lailah labarina” da Mijinta
Tsohuwar jaruma a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Maryam Musa Waziri wadda ke amsa sunan Laila Masu Gonar Naira a tsohon shirin Labarina Series da ya gabata, ta gamu da mummunar hatsarin mota a hanyar Kaduna zuwa Zariya tare da mijinta, Tijjani Babangida wadda tsohon dan wasan kwallon kafar Najeriya ne, da d’an ta Muhammad Fadeel da kuma kanin mijinta, Ibrahim Babangida a ranar Alhamis.
Kanin mijinta, Ibrahim Babangida, shi ya ke tuka motar da su ke ciki lokacin da hatsarin ya faru, wadda kuma a take Allah Ya karbi rayuwar sa, in da aka garzaya da ita kuma Maryam da d’anta da mijinta zuwa Asibiti don kula da lafiyar su.