Bashir Ahmad ya magantu kan rushe masarautun Kano da majalisar dokokin kano nayi
A yau din nan ranar talata majalisar dokokin jihar kano ta rushe masarautun Kano da anka kirkira a karkashin gwamnatin baya ta ganduje wanda dokar da tayi aikin kirkira wadancan itace a yau ta rushe masarautun ta dawo da Masarauta daya tilo a jihar kano.
Bashir Ahmad P.A din tsohon shugaban kasar Muhammadu Buhari yayi martani akan wannan abun da Majalisar dokokin jihar tayi inda yake mai cewa.
“Majalisar Dokokin Kano Ba Ta So Ci Gaban Kano Ba
Hukuncin da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yanke a yau na rushe masarautu biyar da aka kirkira a shekarar 2019 ba karamin koma baya ba ne ga ci gaban jihar ta Kano.
Yawan masarautu a irin wannan zamanin shi ne ci gaba, domin kuwa su masarautun ba su da wani tasiri a kundin tsarin mulkin Nigeria da ya wuce kusanta jama’ar su ga gwamnati.
Jiha kamar Kano bai kamata a ce tana zaune da masarauta daya tilo ba, a yayin da wasu kananan jihohi suke da masarautu da suka wuce 10.
Da Majalisar Dokokin Kano ci gaban Kano suke so, to da kara yawan masarautun ya kamata su yi daga biyar din, ba ma rage su ba.
Ko Gwamnan Kano, zai fi jin dadin tafiyar da gwamnati da sauke nauyin al’umma cikin sauki idan muna da masarautu da dama ba guda daya ba. Domin kuwa wadannan Sarakunan wakilan jama’a ne, kuma za suke tunatar da shi halin da jama’ar su ke ciki, da irin ci gaban da suke bukata a duk lokacin da suka samu ganawa.
A yanzu tunda Majalisar Dokokin Kano tana ganin wadannan masarautu ba ci gaba suka kawowa jama’a ba, zan zama na gaba gaba don kiraye-kirayen ganin an fitar da sabuwar jiha a cikin Kano, musamman daga yankin mu na Kano Ta Kudu, wanda zaman mu a Kano bai tsinana mana komai ba sai koma-baya.
Allah ya kyauta!
Bashir Ahmad, OON.”