Labarai
Ƴan bindiga sun hallaka mutane 24 a jihar Katsina
Advertisment
Kimanin mutane 24 ne aka ce an hallaka tare da jikkata wasu da dama a wani sabon hari da ‘yan bindiga suka kai a Unguwar Sarkin Noma da ke ƙaramar hukumar Sabuwa a jihar Katsina.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito ‘yan bindigar sun kai farmaki a kauyuka hudu a wani mataki da ke nuni da ramuwar gayya kan farmakin da sojoji suka kai maboyar su.
Wadanda abin ya shafa yawancinsu ’yan banga ne wadanda rahotanni suka ce sun fito domin tunkarar maharan.
Wani jami’in tsaron yankin ya shaidawa Channels cewa, harin ya dauki kimanin sa’a guda ana fafatawa.
Ƴan bindigar sun kai farmakin ne a kauyukan Unguwar Sarkin Noma, Gangara, Tafi, da Kore a daren ranar Alhamis da misalin karfe 9:00 na dare.
Dclhausa