AddiniLabarai

Ƙuncin Rayuwa : Jibwis ta nema A fara Alkkunut A Najeriya

Shugaban kungiyar Jama’atu a Jihar Gombe, Injiniya Salisu Muhammad Gombe ne ya bada sanarwar hakan

Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS) ta umurci dukkan masallatanta na Kamsus Salawatna Jihar Gombe da su fara gabatar da Alkunut saboda neman sauki daga tsada da kuncin rayuwa da ake fama da ita.

Shugaban kungiyar Jama’atu a Jihar Gombe, Injiniya Salisu Muhammad Gombe ne ya bada sanarwar hakan.

Ya bayar da umarnin fara Alkunut din ne a taron kungiyar na jiha da ta gabatar da rahoton kwamitin shirya Tafsiri da malamanta suka gabatar a Watan Ramadan.

Shugaban nan take ya bayar da umarni cewa nan take masallatan kungiyar a fadin jihar su fara Alkunut kasancewar rayuwa tamyi tsada jama’a suna cikin kuncin rayuwa.’

Don haka ya ce ya kamata a fara gabatar da al’kunuti ko Allah Zai kawo sauki na wannan bala’in da aka samu kai a ciki.

A taron an tattauna ayyukan da kungiyar ta Izala ta tsara gabatarwa na cigaban addini a yankunan kananan hukumomi 11 na Jihar Gombe.

Sannan cikin farin ciki ya karbi rahoton Malaman da suka gabatar da Tafsiran a wurare sama da 60 a jihar, inda har aka kammala Tafsiran ba a samu wani rahoto marar dadi kan wani Malamin kungiyar Izala ba.

– Aminiya

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button