Labarai

Ƙaddara ko Rashin Imani. : Ya yanka yarinya yar shekaru 4 har sai da ta rasu, bayan garkuwa da ita

Advertisment

Rundunar yan sanda jihar kaduna ta cafke wani matashi mai suna abdulaziz idris da ake zargi da yiwa yarinya yar kawunsa yankan rago bayan yayi garkuwa da ita, yarinya mai suna Aisha dai ta rigamu gidan gaskiya bayan da ya nema kudin fansa Naira dubu dari biyar ₦500,000.

Abdulaziz ya bayyanawa hukumar yan sanda cewa aisha kanwarsa ce bayan ya yanka ta ya jefa gawarta cikin rijiya , abun ya fara a karamar hukumar maƙarfi da ke jihar kaduna.

Bayan nayi garkuwa da Aisha sai na kira yayanta, na sanar da shi cewa kanwarku na hannuna sai yake cemin yanzu babansa baya nan, in bari sai ya dawo, bayan ya dawo munkayi waya.
                     “Mahaifin yarinyar yake cewa shi almajiri ne bai taɓa ganin dubu ɗari biyar ba, bara yake yi, daga nan sai na sake ta,

        sai  yarinyar take  cewa yanzu yaya kai kayi garkuwa da ni ?

Advertisment

Bayan haka sai zuciya ta canza kawai na yanka ta da reza a wuya har ta mutu ” inji abdulaziz idris.

Abdulaziz Idris ya bayyanawa hukumar yan sanda cewa shi magidanci ne matansa biyu ya’yansa biyu amma a lokacin da yake yanka ƙanwarsa Aisha hankalinsa baya a jikinsa.

Bugu da ƙari yace shi baya shaye shaye, ya kara da cewa abin da ya jama sa aikata wannan son zuciya, tsautsayi da karin kwana saboda shi ba halinsa bane.

Kamar yadda zakuji sauran bayyani a cikin wannan faifain bidiyo JKD media na samu rahoton firar da hukumar yan sanya.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button