Labarai

Za mu sake kara farashin lantarki ⁠- Gwamnatin Najeriya

Advertisment

Kwanaki biyu bayan da Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya ta amince da karin farashin lantarki ga kwastomomin da ke karkashin tsarin Band A, gwamnatin kasar ta ce tsugune bata kare ba, domin kuwa akwai yuwuwar karin farashin lantarkin.

Da yake jawabi a wani taron manema labarai a Abuja, Ministan lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce karin kudin lantarki da aka yi a baya-bayan nan wani gwaji ne na kawar da tallafin wutar lantarki a kasar.

Ya ce gwamnati na shirin cire duk wani tallafin da ake bayarwa a fannin domin bayar da damar bunkasa hanyoyin zuba jari a bangaren lantarki.

Ministan ya kara da cewa naira 225 da aka kayyade akan kowanne kilowatt guda ga abokan huldar da ke cikin tsarin Band A ana cajin su kadan ne idan aka kwatanta da naira 500 da suke biya.

Yayin da yake bayyana cewa Najeriya na fama da matsalar game da shirin bayar da tallafi inda gwamnati ke samar da kaso mai yawa na samar da lantarki, la’akari da cewa tana tallafawa da kashi 67 na lantarki, hakan ba karamin koma baya yake haifar mat aba ga bangaren zuwa jari.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button