Labarai

Yan bindiga sun kashe Mai Unguwa, sun kona gidaje, sun yi garkuwa da mutum 20 mata da ƙananan yara a jihar Katsina

Wasu ‘yan bindiga sun kai a garin Na-Alma a yankin karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina, inda suka hallaka mai Unguwa suka kona gidaje, tare da sace sama da mutum 20 mata da ƙananan yara ciki har mata masu juna biyu kamar yadda BBC suka ruwaito.

Katsina Reporters ta samu cewa, lamarin ya faru ne da misalin karfe 8:30pm na daren ranar Laraba wanda daga cikin mutanen da suka sace aƙwai wani dattijo da suka sare ma kafa da hannu a kwanakin baya.

Kwamishinan tsaro na jihar Katsina, Dakta Nasiru Mu’azu ya danganta wannan hari da aka kai garin Na-Alma, da cewa hari ne irin na ramuwar gayya.

Sakamakon halaka wani mutum da ake zargin kasurgumin dan bindiga ne da mukarrabansa, wadanda suka addabi yankin karamar hukumar Malumfashi da kewayenta.

A yanzu dai mutanen yankin sun bayyana cewa suna fuskantar hare-haren ƴan bindiga fiye da kowane lokaci inda kaso tamanin cikin dari na mutanen garin suna cikin rudani.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button