Labarai

Sanadiyar sholisho ya aika ɗan uwansa barzahu

A koda yaushe illa da munin shaye shaye yana kara nuna balai ga al’ummar mu musamman a arewancin nijeriya inda zakaji labarai kala kala akan irin yadda mutane suke kashe mutane akan shaye shaye da suke yake je fasu aikata abinda ba dai-dai ba.

Fitaccen marubucin nan Datti Assalafiy ya wallafa wani labarin mutumin da ya kashe dan uwansa a dai-dai lokacin da ake azamar daukar azumi.

Wannan da kuke gani sunansa Isyaku Babale, yana da shekaru 30 a duniya mazaunin Anguwar Dawaki cikin garin Bauchi

Da misalin karfe 4 na safiyar yau Lahadi wato daidai lokacin da ake shirin daukar azumi Isyaku ya hallaka dan uwansa na jini ta hanyar caka masa wuka a cikinsaSanadiyar sholisho ya aika ɗan uwansa  barzahu

Abinda ya faru shine, Isyaku daki daya suke kwana da yayansa uwa daya uba daya, to a lokacin da ake shirin daukar azumi wato Sahur, sai Isyaku ya tatse Sholisho wanda ‘yan kwaya suke sha zai sha

Shine sai yayansa ya masa fada akan yana damunsa da warin sholisho, to daga nan sai suka fara rigima, sai Isyaku ya zaro wuka ya burma wa yayansa a ciki inda yayi sanadin rasa rayuwarsa

Yanzu haka Isyaku yana kulle a State CID Bauchi, bayan kammala bincike za’a mikashi Kotu domin ya fuskanci hukunci, kamar yadda Maigirma Hazikin Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Bauchi CP Auwal Musa Muhammad ya bada umarni

Yaa Allah Ka shiryar da ‘yan kwaya, Ka karemu daga mummunan kaddara

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button